Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Kasar Iran Rafsanjani Ya Rasu


Hashami Rafsanjani, tsohon shugaban kasar Iran

Gidan talibijin na kasar Iran ya bada sanarwar rasuwar tsohon shugaban kasar, jagaban sauyi Akbar Hashemi Rafsanjani.

Jiya Lahadi Hashemi Rafsanjani wanda yake fama da ciwon zuciya ya rasu yana da shekaru tamanin da biyu a duniya.

Gidan talibijin na kasar ya dakatar da wani shiri da yake gabatarwa domin bada sanarwar rasuwar Rafsanjani

Akbar Hashemi Rafsanjani wanda yayi shugabancin Iran daga alif dari tara da tamanin da tara zuwa alif dari tara da casa’in da bakwai, ana daukar sa a zaman baban mai baiwa shugaban juyin juya hali na kasar marigayi Ayatollah Ruhollah Khomeini shawara.

A wani labarin kuma tsohon shugaban kasar Portugal wanda ya kafa jam’iyar gurguzu ta kasar Mario Soares shima ya rasu yana da shekaru casa’in da biyu a duniya.

Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku daya yau Litinin. Gobe Talata idan Allah ya kaimu za’a yi jana’izar Mr Soares,

A alif dari tara da casa’in da shidda Mr Soares ya zama shugaban kasar Portugal na farko farar hula cikin shekaru sittin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG