Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Paul Kagame Ya Doshi Sake Cin Zaben Rwanda


Paul Kagame
Paul Kagame

Wani jami'in kungiyar Tarayyar Turai (EU) ya fadi a Rwanda cewa da alamar Shugaba Paul Kagame ya doshi sake cin zabe, sannan ya bayyana shakku kan ko EU za ta tura masu saka ido su kula da zaben.

Michael Ryan, shugaban tawagar EU a Rwanda, ya yi magana da 'yan jarida a Kigali jiya Alhamis, kwana guda bayan da wata mace 'yar shekaru 35 wadda aka kashe mahaifinta a wani al'amari mai daure kai, ta ce za ta buga da Kagame a zaben na watan Agusta.

"Ina ganin ba za ka yi asarar kudinka ba, idan ka canki cewa Mr. Kagame zai sake cin zabe," a cewar Ryan a martaninsa ga wata tambayar da Sashin Afirka Ta Tsakiya na Muryar Amurka ya yi.

"Ga Shugaban kasa wanda tabbacin ayyukan da ya yi ke gaban kowa. Sannan kuma ga wasu 'yan takarar da ake jiran su ba da hujjar cancantarsu. Ba a taba gwada su ba kuma sai sun kawo hujja," a cewar sa.

Kagame ya bayar da kyakkyawan Shugabanci na tsawon shekaru 23 ga Rwanda, kuma da dama na ganin shi ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, bayan kisan kiyashin 1994 da ya lakume rayuka wajen 800,000.

To saidai masu suka na cewa Shugabancin Kagame na cike da murdiya da kuma murkushe 'yan adawa. To saidai masu irin wannan ra'ayin tsiraru ne, kuma wasu na ganin saboda farin jinin Kagame ne ma ya sa kungiyar EU ba za ta tura masu saka ido a zaben Rwanda na wannan shekarar ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG