Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Ayyana 12 Ga Watan Yuni A Matsayin Ranar Dimokradiya


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya ya sauya ranar bikin tunawa da Dimokradiya daga 29 na watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin tunawa da Chief Abiola wanda aka yi ikirarin shi ya lashe zaben shugaban kasa na wannan shekarar kafin gwamnatin IBB ta soke zaben

Al’ummar kudu maso yammacin Najeriya sun yi maraba da sauya ranar bikin Dimokradiya zuwa 12 ga watan Yuni maimakon 29 na watan Mayu domin tunawa da gwagwarmayar tsohon dan kasuwa kuma dan siyasa Chief Moshood Abiola.

Shi dai Chief Abiola shi ake ikirarin ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993. Amma gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, ta lokacin ta soke.

A martanin da ta fitar gwamnatin jihar Lagos ta yaba da matakin da shugaba Muhammad Buhari ya dauka a matsayin tukwicin da al’ummar kudu maso yammacin Najeriya da duk masu kaunar Dimokradiya ba zasu taba mantawa dashi ba.

Baicin canza ranar Dimokradiya, kazalika shugaban Najeriya ya ba Chief Abiola lambar yabo mafi girma a kasar. Wani Jimoh Abdullahi cewa ya yi ya ji dadin abun da shugaba Buhari ya yi. Ya ce sun dade suna jiran irin wannan ranar. Matakin, a cewarsa zai taimaka wajen hadin kan ‘yan Najeriya baki daya da sauran masu kaunar tsarin Dimokradiya.

Sauran mutanen da gwamnatin Buhari ta ba lambar yabo sun hada da Chief Gani Fawehinmi da Ambassador Babagana Kingibe wanda ya kasance mataimakin dan takarar shugaban kasa, wato Chief M.K.O. Abiola a zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993 da aka soke

A saurari rahoton Babangida Jibrin

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG