Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Najeriya Ta Ki Tankawa Majalisa


taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba zata mayar da wani martani ba a yanzu dangane da sharudan da Majalisar ‘kasa ta mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Majalisar dai ta mika wasu bukatu guda 12 ga shugaba Muhammadu Buhari, bayan da Majalisar ta yi wani zama akansu kuma take bukakatar shugaban ya aiwatar da su ko kuma su saka kafar wando daya.

Kakakin fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, tun farko ya bayyana cewa ba zasu yi wata magana akan batun ba tukunna, sai dai wata kila a nan gaba. Amma jam’iyyar APC ta fito fili ta bayyana cewa tana daukar mataki na kawo sulhu tsakanin bangarorin guda biyu.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen arewa maso yammacin Najeriya, Inuwa Abdulkadir, ya fadawa Muryar Amurka cewa a jam’iyyance jam’iyya ta siyasa itace uwa, itace uba ga duk wani dan takara, saboda haka dole ne jam’iyyar ta dauki mataki don tabbatar da cewa an sasanta.

Saurari rahotan Umar Faruk Musa domin cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3

Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3-1
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:55 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG