Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fid Da Sabon Tsarin Yaki Da Ta'addanci- Tony Blair


 Tony Blair
Tony Blair

Tsohon Firaministan Burtaniya Tony Blair, ya ankarar jiya Alhamis cewa salon yaki da ta'addanci wanda aka fara amfani da shi tun bayan harin da aka kai Amurka ranar 11 ga watan Satumban 2001 bai yi nasara ba. Blair ya ce ana bukatar wani tsarin da ya fi inganci.

"A takaice abin da na ke son bayyana a sakona na yau shi ne cewa idan aka dubi yawa da kuma tsananin matsalar, ba tare da dakile akida da kuma manufa ba, ba za mu taba yin galaba kan ta'addnci ba," a cewar Blair a yayin wani jawabi a Cibiyar Huldar Kasa da Kasa da ke Washington, inda ya gabatar da rahoton bincikken cibiyarsa ta rajin kawo sauyi a duniya, Global Change.

"Hakika wasu matakan tsaro sun yi amfani ta wasu fuskoki da dama don haka ya kamata a cigaba da amfani da su. To amma maganar gaskiya ita ce dogaro kan matakan tsaro kadai zai jinkirta tashin hankalin ne kawai," a cewar Blair.

Rahoton mai taken, "Global Extremism Monitor: Violence Extremism in 2017," ya gano cewa duk da daukar matakan dakile tsaurin ra'ayin masu ikirarin kishin Islama ta amfani da karfin soji, matsalar sai ma karuwa ta yi bayan 'yan shekaru. Hakazalika, an samu karuwar kungiyoyin ta'adda a 2017.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG