Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Cutar Coronavirus A Najeriya Ya Kai 1,532


Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya wato (NCDC), ta fitar alkaluman sabbin kamuwa da cutar coronavirus (COVID-19) a kasar guda 195. Wannan ya kawo jimlar yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa 1,532.

Sabbin alkaluman sun hada da, 80 daga jihar Lagos, 38 daga jihar Kano, 15 daga jihar Ogun, 15 a jihar Bauchi, 11 a Borno, 10 a Gombe, 9 a Sokoto, 5 a Edo, 5 a Jigawa, da kuam 2 a Zamfara, sai guda daya-daya daga jihohin Rivers, Enugu, Delta, birnin tarayya Abuja da jihar Nasarawa.

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutamne 1,233 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 255 suka samu lafiya, sai mutane 44 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG