Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al-ummar Burundi Za Su Kada Kuri'ar Zabe A Gobe Laraba


Burundi Election Banner 2020
Burundi Election Banner 2020

Al-ummar kasar Burundi za su fita a gobe Laraba don zaben sabon shugaban kasar tare da ‘yan majalisun dokoki, da muma zaben kananan hukumomi, sai dai zaben yana fuskantar kalubale sakamakon annobar coronavirus da zargin tursasawa masu kada kuri’a.

Hakan ya tilasatawa kungiyar kasashen Afrika ta AU da Majalisar Dinkin Duniya fitar da wata sanarwar hadin gwiwa a ranar Lahadi, su na umurtar jami’an tsaro da kafofin watsa labaran gwamnatin kasar, da su ba da gudummuwa wajen ganin dorewar zaman lafiya a cikin kasar, da ake matukar bukata don gudanar da sahihin zabe, da walwalar jama’a.

Zaben na Burundi, shi ne matakin farko da kasar ta dauka na fita daga mulkin shugaban kasar Pierre Nkurunziza wanda ya kwashe tsawon shekaru 15 yana mulki, wanda kuma ke cike da zargin take hakkin bil’adama, da kuma rudanin da kasar ta shiga bayan da ya sanar da sake tsayawa takara neman wa’adin mulki karo na uku na tsawon shekaru 5 da ya jefa kasar cikin mawuyacin halin tattalin arziki.

Janar Evariste Ndayishimiye shine dan takarar shugaban kasa na gaba-gaba karkashin jami’iyyar CNDD-FDD cikin ‘yan takara 6 da ake da su. Ya kuma yi kira ga masu zabe kada su ji tsoron coronavirus, ya na mai cewa Allah na son talakawan Burundi, idan har akwai wadanda suke dauke da cutar haka, hakan ta faru ne domin Allah ya nuna ikonsa a kan Burundi.

Hukumomi a Burundi sun yi watsi da barazanar annobar coronavirus, suka bari ana tarukan siyasa, mutane na walwalarsu yadda suke so.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG