Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido Gidan Gyaran Hali Na Kuje


Buhari ya kai ziyara Kuje.
Buhari ya kai ziyara Kuje.

Shugaban Najeriya ya kai ziyarar gani da ido gidan gyaran halin Kuje cikin wani farin jirgi mai saukar angulu, ya dudduba wuraren da 'yan ta'addan suka dagargaza.

Jami'an hukumar sun shaidawa shugaban kasar cewa, bayan wannan farmaki kimanin daurarru dari takwas da saba'in da tara ne suka tsere. Koda yake Jami'an tsaro sun sake kamo guda dari hudu da arba'in da uku.

NIGERIA-SECURITY/ prison break aftermath - jail fugitives
NIGERIA-SECURITY/ prison break aftermath - jail fugitives

Duk da dai a halin yanzu daurarru dari biyar da hamsin da daya ne ke cikin gidan yarin mai cin mutane dari tara. Yayin da ake neman guda dari hudu da arba'in da uku da suka cika rigarsu da iska.

Gidan gyari hali
Gidan gyari hali

An shaidawa shugaba Buhari cewa fursunoni hudu sun rigamu gidan gaskiya yayinda karin wasu goma sha shida kuma suka Sami raunuka.

Ministan tsaron Najeriya Manjo Jabar Bashir Magashi ya shaidawa 'yan jarida cewa, suna jin yan ta'addan Boko Haram ne suka tafka wannan danyen aiki, domin akwai manyan kwamandojin Boko Haram da ake tsare dasu a gidan, da suka kai sama da sittin da dukansu suka cika rigarsu da iska.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

XS
SM
MD
LG