Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Taro A Kan Kyautata Rayuwar Al'ummomin Yankin Tafkin Chadi


Mawuyacin Halin Da ‘Yan Gudun Hijira Ke Ciki A tafkin Chadi Na Kawo Koma Baya Ga Tabbatar Da Samun Lafiya
Mawuyacin Halin Da ‘Yan Gudun Hijira Ke Ciki A tafkin Chadi Na Kawo Koma Baya Ga Tabbatar Da Samun Lafiya

An gudanar da wani taron wuni a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijer da nufin bitar halin da ake ciki a game da ayyukan farfado da al’amuran yau da kullum a yankin tafkin Chadi wanda ke kokarin murmurewa daga matsalolin Boko Haram da na canjin yanayi.

Taron wanda hukumar MDD mai kula da ayyukan jinkai (OCHA) ta shirya shi tare da hadin gwiwar kasashen Norway da Jamus lokaci ne na tattara karin kudaden da za a yi amfani da su domin inganta rayuwar jama’a.

Ganin yadda kura ta lafa sosai a wurare da dama na yankin tafkin Chadi ya sa gwamnatocin kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa da hukumar MDD mai kula da ayyukan jinkai OCHA suka bukaci tallafin masu hannu da shuni domin farfado da harkokin yau da kullum, mafarin bullo da wannan shiri a shekarar 2017 saboda haka taron na Yamai ke farawa da yin waiwaye inji ministan ayyukan jin kan Nijer Alhaji Lawan Magaji.

Jihohin Yobe, Borno da Adamawa ne yankunan da suka dandani kudar matsalolin Boko Haram a Najeriya inda garuruwa da dama suka watse sanadiyar wannan masifa.

Makwafatakar kut da kut da jihohin arewa maso gabascin Najeriya ta yi sanadin yaduwar rikicin Boko Haram zuwa jihar Diffa a nan Nijer inda dubun dubatar mutane suka tsincin kansu cikin yanayin ukuba.

Wakilin sarkin Bosso, Abba Gana Wakil ya zo da shawarwarin da yake fatan ganin taron ya yi la’akari da su in da ya ce ba za a iya mai da jama'a gidanje su, idan har babu abubuwan more rayuwa, kaman su makarantu, asibiti da dai sauransu.

Da yake wani bangare na wannan zama zai maida hankali wajen tattara kudaden dorewar ayyukan da aka sa gaba tuni wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka yi alkaura.

A cewar hukumar raya tafkin Chadi, ‘yan Najeriya sama da miliyan 1 da dubu 900 ne suka arce daga matsugunsu yayin da abin ya shafi wasu mutun dubu 436 a Cameroun sannan a Chadi mutane dubu 312 da ‘yan kai ne suka yi hijira kamar yadda a Nijer abin ya tilastawa mutane dubu 229 da ‘yan kai ficewa daga matsugunansu a wani lokacin da ake fama da matsalolin canjin yanayi.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
XS
SM
MD
LG