Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Kasuwanci Na Bai Daya Na AFCFTA Zai Habaka Ciniki Tsakanin Kasashen Afirka - Akufo-Addo


Akufo Addo
Akufo Addo

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya bukaci kasashen nahiyar Afirka da su yi amfani da damar da ke cikin sashin gudanar da cinikayya tsakanin kasashen Afirka mara shinge (AfCFTA) don habaka kasuwancin tsakanin Afirka.

Shugaban ya fadi haka ne ranar karshe na taron kwanaki uku da ya hada shugabannin gwamnatoci na Afirka da shugabannin 'yan kasuwa da na masana'antu domin yin musayar ra'ayoyi kan yadda za a bunkasa ci gaban nahiyar Afirka.

Taron da aka yi wa taken: ‘Daga Buri Zuwa Aiki – Isar da Wadata ta Hanyar Cinikayya a Nahiyar’. Bayan masu jawabai sun gudanar da jawabansu, daya bayan daya kan yadda Afirka da ke da dimbin arziki za ta fidda kan ta daga cikin kangin talauci.

Maitamakin shugaban kasar Ghana Bamwumia
Maitamakin shugaban kasar Ghana Bamwumia

Shugaba Akufo-Addo, kuma babban bako mai jawabi a wajen rufe taron, ya ce matakin da wasu kasashe 44 suka dauka, na shiga yankin gudanar da cinikayya nahiyar Afirka mara shinge (AfCFTA) ya nuna karara cewa, nahiyar a shirye take ta yi kasuwanci a tsakaninta. Ya yi alkawarin cewa zai tattauna da sauran kasashen Afirka 10 da suka rage domin tabbatar shigar dukkan kasashen Afirka.

Ya ce: “Abin farin ciki ne a lura cewa, ya zuwa watan Nuwamban shekarar 2022, mambobin kasashe 44 sun amince da AfCFTA, wannan wata kwakkwarar shaida ce da ke nuna ci gaban siyasa da jajircewar shugabannin nahiyar, wajen cimma hadakar kasuwanni a Afirka. Kuma ya zama wajibi mu hada hannu don tabbatar da kasancewar dukkan kasashen nahiyar suna ciki.”

Hamza Adam Attaijjany, mai sharhi kan tattalin arziki ya bibiyi wannan taro kuma ya yi wa Muryar Amurka karin bayani. Ya ce, hukumar AfCFTA na bukatar shugabannin kasashen Afirka da su sassauta haraji da kashi 70 cikin 100 domin samun sauki ga ‘yan kasuwa. Kuma, Afirka ta iya sarrafa albarkatun kasa da take da su yadda za a samu farashi mai kyau idan an fidda su zuwa kasashen waje. Haka kuma ya kamata a samu yadda za a magance fidda kudi daga Afirka ba bisa ka’ida ba, domin Afirka na asarar Dalar Amurka biliyan 88 duk shekara a sanadiyar hakan.

A rana ta biyu ta tattaunawar, mataimakin shugaban kasa, Dokta Mahamudu Bawumia, a jawabinsa ga ministoci, jakadu da ‘yan kasuwan Afirka, ya yi nuni da cewa, ya kamata nahiyar ta yi kokarin ganin ta magance gibin ababen more rayuwa da ake bukata domin saukaka aiwatar da shirin na AfCFTA, wanda zai iya cin kudin da ba zai gaza dalar Amurka biliyan 130 a duk shekara.

Ya ce: “Afirka na bukatar kimanin dalar Amurka biliyan 130 zuwa biliyan 170 a duk shekara domin toshe gibin ababen more rayuwa a nahiyar, a kashi 5 cikin 100 a kowace shekara ko fiye da haka. Wannan yana ba da damammaki masu yawa don saka hannun jari a kamfanoni masu zaman kansu, ”

Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Issah Mairago Gibril Abbas ya yi kira ga shugabannin da suka yi wannan zaman tattaunawa da su tabbatar da matsaya da suka dace.

Saurari rahoton Idris Abdullah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

XS
SM
MD
LG