Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Hukuncin Kotun Kolin Najeriya Kan Ci Gaba Da Amfani Tsofaffin Takardun Kudi


Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

A ranar 3 ga watan Maris ne kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za’a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudaden N200, N500 da N1000, da babban bankin kasar na CBN ya sauya fasalinsu har ya zuwa karshen wannan shekara, wato 31 ga watan Disamba.

Babban bankin na CBN ya ba da sanarwar sauya fasalin kudin ne a cikin watan Oktoba da ya gabata, inda kuma ya fitar da sababbin takardun kudin a cikin watan Disamba, kana kuma da farko aka bai wa ‘yan kasar wa’adin 31 ga watan Janairu, da kowa ya canja kudinsa kafin lokacin, sa’adda tsofaffin takardun kudin za su kare aiki.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

To sai dai wa’adin bai gamsar da ‘yan kasar ba, sakamakon wahalhalu da karancin sababbin takardun kudin, lamarin da ya sa aka kara wa’adin.

Wasu gwamnoni sun garzaya zuwa kotun koli tare da bukatar kotun ta tilastawa bankin CBN da gwamnatin tarayya dakatar da sabon tsarin, wanda suka ce ya jefa ‘yan kasar a cikin mawuyacin hali.

A cikin hukuncin nata, kotun kolin ta kafa hujja da cewa ba’a baiwa ‘yan Najeriya sanarwa cikin cikakken lokaci ba kafin soma aiwatar da shirin, haka kuma bayan soma aiwatar da shi, ba’a samar da isassun takardun kudaden da za su maye gibin tsofaffin kudaden ba.

Kotun Kolin Najeriya
Kotun Kolin Najeriya

To sai dai a yayin da ‘yan Najeriya da dama suka yi na’am da hukuncin kotun kolin, bisa fatar ganin an sami sauki kan wahalhalun da karancin takardun kudaden ya haifar, wasu da daman a ganin cewa har yanzu ba abin da ya sauya, duk kuwa da hukuncin na kotun koli.

Hasali ma wasu ‘yan kasar na cewa hukuncin “ya haifar da rudani a kasar, yayin da gwamnatin tarayya ko bankin na CBN suka ki cewa uffan kan bin umarnin kotun kolin ko akasin haka.”

“Kamar yadda ake cewa (shugaba Buhari) mai biyayya ne akan ko wane umarnin kotu, kuma yana son bin ka’ida, to a gaskiya wannan karon muna son mu gani a kasa, yayi biyayya ga umarnin kotu” in ji wani dan Najeriya mazauni jihar Borno da ke Arewacin kasar.

Ya ci gaba da cewa “daya daga cikin manyan matsalolin da suka fi damun mu a halin yanzu ma shi ne matsalar rashin lafiya. Idan ka je asibiti sai su ce dole zaka biya kudi kasa ba za su karbi turawa ta asusun banki ba.”

Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)
Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)

Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami, a wata zantawa da Muryar Amurka bayan hukuncin kotun kolin, ya bayyana cewa suna nan suna nazari tare da bin bahasin hukunci kafin daukar mataki a kai, to amma bai yi takamaiman bayanin ko gwamnati za ta yi biyayya ga umarnin na kotu ba, ko kuma tana nan kan matsayin ta na wa’adin 10 ga watan Afrilu da shugaba Buhari ya ba da sanarwa a wani jawabi da yayi wa ‘yan kasar kan lamarin.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu:

XS
SM
MD
LG