Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar HURIWA Ta Bukaci Shugaba Buhari Da Emefiele Su Yi Murabus Saboda Karancin Naira


Shugaban kungiyar HURIWA Mr. Emmanuel Onwubiko
Shugaban kungiyar HURIWA Mr. Emmanuel Onwubiko

Bayan kwanaki da kotun koli ta ba da umurni akan tsofaffi da sabbin kudin Naira, gamayyar kungiyoyin marubata kan kare hakkokin bil’adama wato HURIWA, ta yi kira ga shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya ajiye aiki.

HURIWA ta ce har yanzu ana korafi a kan karancin kudi da kuma yadda fadar shugaban kasa ta yi shiru bata ce komai ba akan umurnin kotun kolin.

Wannan dai wani kokari ne na kungiyar HURIWA, na ganin an yi biyayya ga umurnin kotun koli wanda ya tsawaita wa'adin halascin amfani da kudin zuwa karshen wannan shekarar ta 2023.

A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Emmanuel Onwubiko, wadda aka ba manema labarai, kungiyar ta koka kan irin halin ko in kula da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, da shugaba Buhari suka yi wa umurnin kotun kolin, inda ya ce sun gallaza wa ‘yan Najeriya azaba kan rashin kudi bayan da suka sauya fasalin Naira 200, 500 da 1,000. Onwubuko ya ce wadannan manyan shugabannin biyu sune suke tafiyar da kasar yadda suke so ba tare da tausayin halin da ‘yan kasa suke ciki ba. Onwubiko ya kuma ce kungiyar bata yarda da irin wannan mataki da zai sake ruguza tattalin arzikin kasar ba, saboda haka yana kira ga Emefiele da Buhari da su sauka daga mukamansu domin sun gaza.

Kudin Naira
Kudin Naira

Amma ga masanin tattalin arziki na kasa-da-kasa Yusha'u Aliyu, ya ce in an bi tsarin da kyau, sauya kudin na da muhimmanci kuma zai iya zama Alheri ga kasa.

Yusha'u ya ce dole ne sauya kudaden kasa ya zama abin da zai daidaita tattalin arzikin kasa kuma kudin na kasa ne, da ya zama dole ‘yan kasa su yi mu'ammala da su, wato suna canja hannu tsakanin al'umma wajen biyan bukatu a kasar. Yusha'u ya ce wannan hada-hada ita ce hanyar inganta tattalin arzikin kasar.

Amma wata ‘yar kasuwa mai shagon gyara wa mata gashi a Abuja Nkechi Okolie, ta ce a daidai wannan lokacin matakin bai yi mata dadi ba, domin akwai matsala wajen samun tsoffin kudaden a bankuna. Nkechi ta ce bayan ta samu kudin ma, ba ta iya ciniki da su ko ta kashesu domin ba a karbar su a kasuwanni.

Nkechi ta ce kawai abin da ya fi a'ala shi ne, gwamnati ta dauki matakin fito da sabbin kudaden da yawa domin ‘yan kasa su samu. Ta kara da cewa wahala mutane suke sha sosai a kasar akan karancin kudi.

Naira dubu daya
Naira dubu daya

Daya daga cikin 'ya'yan kwamitin wucin gadi da majalisar wakilai ta kafa kuma shugaban kwamitin kula da bankuna, Inshora da hada-hadar kudi Hafiz Kawu, ya ba da shawarar cewa hanya daya ce babban bankin Najeriya zai dauka da zai kawo wa mutane sauki a yanzu, hanyar kuwa ita ce CBN ya fito da kananan kudade irin su Naira 100, 50, 20 da kuma na kasa da haka, wadanda cajin fasalin Naira bai shafesu ba, don kawo wa mutane sauki.

Hafiz ya kara da cewa ya kamata matasa su shiga kasuwancin POS domin kawo sauki a hada-hadar kudi, yanzu ana da mutane miliyan daya da dubu dari uku da suka shiga harkar POS.

Kungiyar ta ce ya kamata a yi hanzarin daukar matakin soke duk tsare-tsaren da wannan gwamnati ta kawo domin ta riga ta yi wa kasar illa.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

XS
SM
MD
LG