Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Lamunin Dala Biliyan 3 Da Ghana Ta Samu Daga IMF Zai Magance Matsalolinta? - Masana


hukumar lamuni ta duniya IMF
hukumar lamuni ta duniya IMF

Bayan gwamnatin Ghana ta yi nasarar samun bashin dala biliya uku da hukumar lamuni ta duniya IMF, manzarta a kan harkokin kudi da tattalin arziki a kasar na tsokaci a kan makomar wannan bashi da aka ciyo, yayin da wasu ke dora ayar tambaya a kan yarjejeniyar bada bashin.

Dan majalisar dokoki mai wakiltar Tamale South, Haruna Iddrisu shima ya nuna damuwa da wani bangare na yarjejeniyar da gwamnatin Ghana ta kulla da asusun lamuni na duniya (IMF).

Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai matukar buri, duba da wasu sharuddan da aka sanya.

“Ni dai a gani na yarjejeniyar IMF da gwamnatin Nana Addo Dankwah Akufo-Addo da Bawumia suka sanya wa hannu, wani abu ne da ya wuce gona da iri. Saboda zai yi tasiri a kan kasafin kudi na sabuwar gwamnati mai jiran gado. Mai yiwuwa gwamnatin John Mahama ce da gwamnatin NDC gobe,” in ji shi yayin da yake tattaunawa da gidan rediyon Joy FM.

A ranar Laraba ne dai kwamitin zartarwa na asusun lamuni na IMF ya amince da shirin bayar da lamuni na dala biliyan 3 ga Ghana na tsawon shekaru uku, wanda zai ba da damar cire kusan dalar Amurka miliyan 600 nan take, lamarin da ake ganin zai fidda kasar ta Afirka ta Yamma cikin mawuyacin halin tattalin arzikin na tarihi da kasar ke fama da shi.

A cikin wata sanarwa da IMF ta fitar ta ce, tabbatar da yarjejeniyar sake fasalin basussukan cikin lokaci tare da masu ba da lamuni na waje zai zama muhimmin batu wajen samun nasarar aiwatar da lamunin da nufin taimakawa Ghana shawo kan manufofin nan da nan da kalubalen samar da kudade.

Asusun ya kuma ce sabon lamunin zai taimaka wajen tattara karin kudaden waje daga abokan huldar ci gaba tare da samar da tsarin kammala sake fasalin bashi.

"Ina taya Ghana murna da wani gagarumin shirin sauye-sauye don farfado da ci gaban da kuma rage yawan basussukan da ake bin kasar," in ji Manajan Daraktar IMF Kristalina Georgieva a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter.

Georgieva ta ce, alkawarin da bangarorin biyu suka yi na taimakawa Ghana ta ci gaba da dorewar kan basussukan da ake bin kasar, na nuni da muhimmin ci gaba ga tsarin bai daya na kungiyar G20 da ta dade tana yafe basussukan kasashe masu tasowa.

Majiyoyin da ke da masaniya kan sabon shirin na Ghana sun yi gargadin cewa mahukunta a can sun fuskanci doguwar tattaunawa da masu bada bashi, inda suka yi nuni da kasar Zambia, da irin wannan tsari da ya samu tsaiko.

XS
SM
MD
LG