Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ware Naira Biliyan 150 Domin Yaki Da Talauci


Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ware zunzurutun kudi har naira bilyan 150 domin aiwatar da tsare-tsarenta na yaki da talauci a shekarar 2024.

Za’a kashe kudaden ne karkashin ginshikan daidaita tattalin arzikin kasa guda 4 da suka hada da; bunkasa masana’antu da samar da sauye-sauye a manufofi da tsare-tsare da yin garanbawul a hukumomi da manufofin rabon arziki da tsare-tsaren gwamnati karkashin tsarin Yaki da Talauci da Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa.

Baya ga warewa shirin gwamnatinsa na yakar talauci da bunkasa tattalin arziki, a kasafin naira tiriliyan 28 da biliyan 770 daya rattabawa hannu, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya warewa Ma’aikatar Jin Kai da Yaki da Talauci naira biliyan 10 da miliyan 350.

Majalisar Zartarwa ta Kasa ce ta amince da shirin Yaki da Talauci da Bunkasa Arziki a shekarar 2021 a wa’adin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da nufin magance talauci, musamman a yankunan karkara.

An tsara gudanar da shirin ne a cikin shekaru 10 tsakanin shekarar 2021 zuwa 2031, inda aka kiyasta cewar shirin zai lakume dalar amurka tiriliyan 1 da bilyan 600 idan ana kashe kimanin dala bilyan 161 a duk shekara.

Dab da zata mika ragamar mulki ga gwamnatin Bola Tinubu, gwamnatin Shugaba Buhari tayi ikirarin cewar jumular talakawa miliyan 1 da dubu 800 suka ci gajiyar shirin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG