Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Charles Taylor Zai Gurfana Gaban Kotun Bin Kadin Laifuffukan Yaki Ranar Litinin


A ranar litinin, tsohon shugaban kasar Liberiya, Charles Taylor, zai bayyana a karon farko gaban kotun bin kadin laifuffukan yaki mai samun tallafin Majalisar Dinkin Duniya, MDD.

Jumma'ar nan ce Kotun ta Musamman ta Saliyo ta bayar da sanarwar cewa za a gurfanar da Charles Taylor a gaban kotun alkali Richard Lussick.

Majiyoyi na kusa da kotun sun ce za a karantawa Taylor irin laifuffukan da alke zargin ya aikata, sannan sai a bukace shi da ya yarda ko rashin yardarsa da aikata su.

Kotun tana tuhumar Taylor da aikata laifuffuka goma sha daya na yaki da na cin zarafin bil Adama, dukkansu wadanda suka samo asali daga rawar da aka ce ya taka a mummunan yakin basasar kasar Saliyo.

An damke Taylor aka mika shi hannun kotun a ranar laraba, a bayan da Nijeriya, wadda ta ba shi mafaka a 2003, ta bayyana amincewarta da kama shi.

Kotun ta bukaci kasar Netherlands ta dauki dawainiyar gudanar da shari'ar a can, tana mai fadin cewa gudanar da wannan shari'a a Saliyo zata iya haddasa fitina a cikin kasar da kuma a Liberiya.

Kotun ta ce ita ce zata gudanar da shari'ar a can Netherlands, inda take fatar yin amfani da kayayyakin kotun duniya dake birnin Hague.

Hukumomin kasar Netherlands su na tattauna yadda za a kai Mr. Taylor can, sun kuma bukaci Kwamitin Sulhun MDD da ya zartas da kudurin da zai amince da sauya wurin da za a yi shari'ar ta Mr. Taylor

XS
SM
MD
LG