Tsohon shugaban kasar Liberiya, Charles Taylor, ya ki amsa laifuffuka 11 da ake tuhumarsa da aikatawa a gaban kotun bin kadin laifuffukan yaki a kasar Saliyo.
A bayyanarsa ta farko a gaban kotun a yau litinin, kuma kafin ya bayar da amsa game da tuhumar tasa, Mr. Taylor ya ce bai yarda da hurumin kotun ba.
Ya kara da cewa laifuffuka 11 da ake tuhumar ya aikata, ci gaban yunkurin da ake yi ne na rarraba kawuna tare da mulkin al'ummar kasashen Liberiya da Saliyo.
Tuhume-tuhumen sun samo asali daga goyon bayan da aka yi zargin ya bai wa 'yan tawayen Saliyo, wadanda aka yi zargin sun aikata munanan laifuffuka na cin zarafin bil Adama a lokacin yakin basasar kasar.
Wani lauyan da kotun ta nada ne ya wakilci Taylor a zaman yau, wanda aka yi cikin tsaro sosai.
Iyalan Mr. Taylor sun ce ba su tsammanin za a yi masa shari'a ta adalci a kasar Saliyo. Kotun ta nemi dage shari'ar zuwa kasar Netherlands, tana mai fadin cewa kasancewar Taylor a Saliyo tana iya haddasa fitina a kasar da kuma a Liberiya.