Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Liberiya Charles Taylor Yana Shirin Bayyana A Gaban Kotun Bin Kadin Laifuffukan Yaki Ta Saliyo A Birnin Freetown


Tsohon shugaban kasar Liberiya, Charles Taylor, yana shirin bayyana a karon farko yau litinin a gaban kotun bin kadin laifuffukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya a Freetown, babban birnin Saliyo.

Za a bukaci Taylor da ya amsa, ko kuma ya musanta laifuffuka goma sha daya na yaki da na cin zarafin bil Adama da ake tuhumarsa da aikatawa.

Wadannan tuhume-tuhume su na da nasaba da goyon bayan da ake zargi ya bayar ga 'yan tawayen Saliyo, wadanda aka ce sun aikata munanan laifuffuka a lokacin yakin basasar kasar.

Ana sa ran cewa lauyoyin kariya na kotun zasu wakilce shi a zaman yau, amma kuma an bayar da rahoton cewa Mr. Taylor ya nemi wani lauya na Amurka mai suna Alan Dershowitz, da ya wakilce shi.

Iyalan Mr. Taylor sun ce ba su tsammanin tsohon shugaban na Liberiya zai fuskanci shari'ar adalci a Saliyo.

Kotun ta bukaci da a dage zaman shari'ar zuwa kasar Netherlands, su na masu fadin cewa kasancewar Taylor a Saliyo tana iya haddasa fitina a cikin ita kanta Saliyo da kuma a kasar Liberiya.

A makon jiya, Britaniya ta gabatar da daftarin kuduri a gaban Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bayar ad iznin dage zaman kotun zuwa kasar Netherlands.

XS
SM
MD
LG