Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Hira Da Mawaki Morell Kashi Na Biyu, Satumba 04, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun gabatar da kashi na biyu na hira da mawaki Morell. Mun kuma bada labarin wadansu Goburawa biyu da suka tafi cirani a Lagos, daya yana sana'ar dako gudan kuma yana sana'ar faskare. Da suka isa da dare suna neman inda zasu kwana sai suka yi karo da 'yan sanda suka kuma nemi Goburawan su gaya masu abinda su ka zo yi Lagos. A bayaninsu mai sana'ar dakon ya gayawa 'yan sandan da Sakkwatanci shi sana'ar "dauke-dauke" ya ke yi, gudan kuma mai sana'ar faskare, yace shi sana'ar "fashi" ya ke yi a biya shi.

Saurari cikakken shirin:

A Bari Ya Huce: Hira Da Mawaki Morell Kashi Na Biyu-25: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:25:36 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG