Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Babarbare Da Bafullatani Da Aljani-Octoba, 03, 2020


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Wadansu abokai ne Bafullatani da Babarbare suna tafiya adaji da daddare suna zuwa gidin wata tsamiya sai wani katon aljani ya kama tukkun Bafullatanin ya rike gam shi kuma sai ya tsaya kawai baiyi ihu ba bai fadawa abokin sa ba.

Shiko abokin yana tafiya yayi magana yaji shiru ya waiga baiga abokin sa ba sai ya dawo ya taras da abokin a tsaye yace mashi a’a mallam ya aka yi ka tsaya nan ka bar ni ina ta zuba ni kadai? Sai Bafullatanin yace masa wanin ɗan iskan aljanine ya rike mun tukku shine na tsaya inga abinda yake nufi da bata min lokaci.

Bude bakin Babarbaren sai yace to bari in hau bishiyar inga wane karamin ɗan iskan aljanine ya rike ka

Aljani na jin haka sai ya saki Bafullatani. Sai Bafullatanin ya cewa abokin af bari ma tsinannan ya sake ni, mu yi tafiyarmu.

A cikin wadannan mutanen biyu wa ya fi jarumtaka?

A BARI YA HUCE: Labarin Babarbare Da Bafullatani Da Aljani-28:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:29:34 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG