Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Mahauci a Barikin Soji-Fabrairu, 12, 2022


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A shirin A Bari Ya Huce na wannan makon, mun kawo maku labarain wani Mahauci da ya dade yana kaiwa kwamandan Sojoji nama a barikin soji kuma su ka saba sosai da sojojin da ke gadi a bakin get din shiga barikin. Wata rana Mahaucin ya je kai nama a maimakon bin ta inda ya saba sai ya bi yanke yana sauri ashe ya shiga inda bai kamata farin kaya ya shiga ba. Da hango shi sai sojoji su ka daka mashi tsawa su ka ce ya tsaya. Da farko ya yi watsi da su domin bai zaci za a tsayar da shi ba da yake ya saba shiga barikin, da ya gane lallai shi ake wa magana ya tsaya. Da isowar sojojin sai ya bushe da dariya yana cewa, yallabai baku gane da ni ba ne? Kafin ya rufe baki sai wani ya kara daka mashi tsawa ya ce a ajiye kunshin naman ya tsaya can gefe.

Saurari cikakken shirin ka ji yadda ta kaya:

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG