Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Yaro Mai Neman Karin Tuwo Da Mahaifiyarsa-Yuli,17, 2021


Alheri Grace Abdu

A shirin mun karbi bakuncin fitaccen mawakin Hausa da ake kira Musicman.

Mun kuma bada labarin wani yaro wanda duk lokacin da aka gama abinci aka basu suka ci, sai mahaifiyar su ta tambaye su ko sun koshi ko a kara masu,
sai yace bai koshi ba a kara mashi. Kullum kafin a kara masu sai mahaifiyar tace mashi kai dai baka da godiyar Allah. Kullum haka har ta kai yaron nan ko da bai koshi ba idan mamar tasu tace sun koshi sai yace ya koshi saboda kada tace bashi da godiyar Allah.

Wata rana suna cin abinci tare da uwar bayan sun cinye sai mahaifiyar
ta tambaye su, ko sun koshi, sai yace ya koshi sai uwar tace ni dai ban koshi ba. Sai yaron ya kalle ta yace kai mama ba ki da godiyar Allah. Maganar da yaron ya yi ta dame ta sosai.

Saurari cikakken shirin:

A Bari Ya Huce: Labarin Yaro Mai Neman Karin Tuwo Da Mahaifiyarsa-23: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:48 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG