Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Bauchi Sojoji Sun Kashe Wasu Bata Gari Hudu


Biyo bayan labarin da aka ba sojojin dake cewar wasu bata gari sun boye a dajin Lamibura suna shirin kai hari a garin Diwa domin aiwatar da ta'adanci

Mutanen da suka gamu da karshen rayuwarsu a wani shirin kwantan bauna da sojoji suka yi masu an ce suna sace mutane ne tare da yin fashi da makami kuma abun da zai kaisu garin Diwa ke nan.

Mukaddashin daraktan yada labaru na rundunar sojojin Najeriya Kanar Sani Kukasheka shi ya yiwa Muryar Amurka karin bayani. Yace sun samu labari daga mazauna yankin cewa wasu bata gari sun shiga dajin suna shirin kai hari a garin Diwa. Yace sojojinsa sun yi gumurzu da mutanen kafin su samu nasarar hallakasu duka.Baicin kashe mutanen sun samu makamansu da suka hada da bindigogi da adduna da layu.
Dan majalisar da ya fito daga yankin ya yabawa sojoji da sauran jami'an tsaro. Yace zasu cigaba da kasancewa a yankin har sai an kawar da miyagun mutane.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Bidiyo

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG