Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Taka Rawa A Harin Mosul In Ji Janar Townsend


Janar Stephen J. Townsend
Janar Stephen J. Townsend

Kwamandan sojojin Amurka dake Iraqi, Janar Stephen Townsend, yace a saboda dakarun Amurka sun kai hari a yankin da fararen hular suka mutu, a bisa dukkan zato wannan harin ne ya haddasa mutuwarsu.

Kwamandan sojojin Amurka a kasar Iraqi, yace a bisa dukkan alamu sojojin na Amurka sun taka rawa a wani hari ta sama da aka kai a Mosul, harin da shaidu suka ce ya kashe fararen hula kimanin dari daya a ranar 17 ga watan nan na Maris.

"A saboda mun kai hari a wannan yanki, ina kyautata zaton cewa mune muka haddasa mace-macen" in ji Leftana Janar Stephen Townsend a lokacin da yake tattaunawa da 'yan jarida ta wayar tarho daga birnin Bagadaza a yau talata.

Kwamandan dake jagorancin yaki da kungiyar Daesh a Iraqi da Syria, yace shugabannin soja na Iraqi sun yi imanin cewa mayakan kungiyar Daesh ko ISIS sune suka tattara wadannan fararen hula a wurin kafin wannan harin, ko dai don dana tarko ma sojojin kawance wanda zai kai ga kashe fararen hular, ko kuma domin suyi amfani da su a zaman garkuwa.

Yace, "Mun san mayakan Daesh suna fada daga wannan wurin, daga wannan ginin, kuma akwai mutanen da ba zaka iya sanin me ya kai su wurin da ake harbe-harbe ba, sai dai watakila ko an tilasta musu ne."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG