Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Cikin Masallatan Juma'a Aka Gudanar Da Sallah Eid Fitr A Taraba Da Adamawa


A jihohin Adamawa da Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya an gudanar da sallar Eid Fitr ne a cikin tsauraran matakan tsaro da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Ba kamar sallar shekarar data gabata ba, a bana an gudanar da sallar idi ne a massalatan Jumma’a maimakon filin idi,sakamakon ruwan da aka tafkawa kamar da bakin kwarya musamman a Yola da Jalingo.

Duk da hakan hukumomin sun tabbatar da ganin cewa matakan tsaron da aka dauka domin tabbatar da ganin cewa an gudanar da bukukuwan sallah sun yi tasiri.

Wannan yanayi da aka tashi dashi yasa a bana ba’a gudanar da hawan gaisuwar sallah ba da akan yi a fadar manyan sarakunan jihohin biyu.

Kamar magidanta suma yara kanana ba’a barsu a baya ba a shagulgulan sallar inda suka nuna farin cikinsu, koda yake yayin da wasu ke kokawa, wasu ‘yan majalisu sun tuna da jama’ar su a wannan karon.Hon. Sulieman Alkali shike wakiltar mazabar Yola ta arewa a majalisar dokokin jihar Adamawa ya bada kayakin tallafi a mazabarsa da suka hada da shanu.

Tun farko dai gwamnan jihar Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya yiwa al’umman jihar fatan alheri.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG