Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Fara Duban Wata Da Yammacin Litinin, A Dakata Da I’tikafi – Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar.
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar.

Sanarwar ta ce, “idan har Musulmi amintattu suka ga watan, Mai Alfarma zai sanar da a fara azumi a ranar Talata 13 ga watan Afrilu. Idan kuma aka samu akasin hakan, ya zama Laraba 14 ga watan Afrilun 2021, za ta zama ranar azumin farko.”

Majalisar koli ta malaman addinin Islama NSCIA da ke karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar, ta yi kira ga al’umar Musulmin kasar da su fara duban jinjirin watan Ramadana daga yammacin ranar Litinin.

Majalisar ta fitar da sanarwa ce a shafinta na Twitter a ranar Lahadi inda ta nemi jama’a da su saurari sanarwar ganin watan.

“Tare da shawarar kwamitin duban wata na majalisar, shugaban majalisar na yin kira ga al’umar Musulmi, da su fara neman jinjirin watan Ramadana da zarar rana ta fadi a ranar Litinin 12 ga watan Afrilu 2021, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Sha’aban 1442 bayan hijira.” Sanarwar ta ce.

Karin bayani akan: Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar, Ramadana, COVID-19, Nigeria, da Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, “idan har Musulmi amintattu suka ga watan, Mai Alfarma zai sanar da a fara azumi a ranar Talata 13 ga watan Afrilu. Idan kuma aka samu akasin hakan, ya zama Laraba 14 ga watan Afrilun 2021, za ta zama ranar azumin farko.”

Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga al’umarsa, da su kiyaye ka’idojin da aka saka na kare yaduwar cutar COVID-19 a lokacin da suke duban jinjirin watan, sannan su kuma dakata da shiga I’tikafi da tsawaita taruka saboda annobar.

Wannan shekara, ita ce ta biyu da za a yi azumin Ramadana yayin da duniya ke yaki da annobar korona wacce ta faro daga karshen shekarar 2019.

XS
SM
MD
LG