Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Faransa Jami'ai Na Shirin Ruguje Wani Sansanin Yan Gudun Hijira


Sansanin Yan Gudun Hijira kusa da garin Calais a Faransa

Jami’ai a Faransa suna shirin rosawa da kuma tada dukkan mutanen dake cikin wani sansanin yan gudun hijira da ke kusa da birnin Calais mai tashoshin jiragen ruwa dake Arewacin kasar.

Aikin kwashe ‘yan bakin haure da yawansu ya kai akalla 6,486 - kungiyoyin agaji sun ce kila ma yawan mutanen zai kai 8,300 – ana jin zai dauki kamar mako guda ana yinsa.

Za a baiwa bakin hauren wuraren zama a cibiyoyin yan gudun hijira a fadin kasar Faransa da kuma daman neman mafaka.

Sai dai akwai damuwar cewar wasu bakin hauren ba zasu yarda su tashi daga wurin ba saboda zasu nemi ketarawa zuwa Birtaniya ta wannan hanyar.

Birtaniya ta riga ta fara karban wasu kananan yara da yawansu ya kai 1,300 dake zaune a sansanin su kadai ba tare da iyayensu ba.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG