Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Mayar Da Hankali Wajen Yakin Neman Zabe


Hillary Clinton

‘Yar takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin jami’iyar Democrats Hillary Clinton wacce ke kyautata zaton lashe zaben da za’a yi a watan gobe, yanzu tayi watsi da abokin karawarta na Republican Donald Trump, kuma ta mayar da hankali wurin yakin zaben wakilan jami’iyarsu don samun rinjayi a manyan majalisun dokokin tarayya na Amurka din.

Hilary ta gayawa manema labarai cewa yanzu bata ma tunanin mayar wa Trump da martini kuma, a kan sukar lamirin da yake yi mata na cewa ita mai karbar rashawa ce don haka bata cancanci shiga fadar shugabancin Amurka ta White House ba.

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta shaidawa yan jarida a cikin jirgin kempen nata a shekaranjiya Asabar, cewa tana kyautata zaton itace zata zama shugaban Amurka mace ta farko, tace sauran kwanaki 16 da suka rage a yi zaben na ranar takwas ga watan Nuwamba, zata mai da hankali ne wurin ganin an zabi masu yiwa Democrat takarar majalisa don su samu rinjayi a nan majalisar, wanda a halin yanzu Republican ce ke da rinjayi a duka majalisun biyu na wakilai da ta Dattawa.

Clinon, wacce dukkan ra’ayoyin jama’a da ake dauka ke nuna cewa tafi Trump yiyuwar lashe zaben, yanzu haka ta karkatar da miliyon dololi na kempen nata zuwa jihohi da Republican ke yawan lashe zabukan shugaban kasa a kokarin da take yi na kara yawan kuru’u da zasu bata babban galaba a kan Donald Trump da kuma ganin masu takarar majalisa karkashin tutar Democrat sun doke yan Republican dake rike da kujerun jihohin.

Masu sharhi sun ce ‘yan jam’iyyar ta Democrat zasu iya kwace rinjayi a majalisar dattawa, amma dai zaiyi matukar wahala su kwato Majalisar wakilai daga hannun ‘yan Republican.

XS
SM
MD
LG