Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Nijar Wasu Na Ganin Shugaban Amurka Ya Fara Wuce Gona da Iri


Shugaban Amurka Donald Trump

Lura da matsayin da Amurka take dashi a duniya saboda jajircewarta a wajen takawa kasashen dake kaucewa dokokin kasa da kasa birki ya sa jama'a nuna adawa da matakin shugaba Donald Trump na hanawa 'ya'yan wasu kasashe bakwai na musulmi shiga kasarta Amurka saboda zarginsu da aikata ta'adanci.

Shugaban kungiyar kare hakkin Bil Adama Alhaji Mustapha Kadi Ummani yace sabon shugaban na Amurka, wato Donald Trump ya fara wuce gona da iri.

Inji Kadi Ummani kasar Amurka ba amurkawa kawai ke da 'yancin morarta ba. Idan ma aka bi sassala da gumin afirkawa aka gina kasar.

Yana mai cewa Donald Trump ya fara wuce gona da iri domin duk wanda yake shugaban Amurka nauyin sauran kasashen ya rataya a kansa. Yanzu babu kasar da zata iya rayuwa ba tare da wata ba saboda haka suna kira gareshi ya sake duba wasu matakan da ya dauka. Suna kira ya tuna Amurka ba ita kadai ba ce a duniya, akwai wasu.

A cewar Alhaji Ummani arzikin Amurka ya ta'allaka ne akan bautar da 'yan asalin Afirka suka yi a kasar kafin yau ta zama abun da ta zama. Saboda haka mutanen Afirka suna da alhaki a Amurka. Haka ma mutanen Asiya suna da alhaki a Amurka.

A sakamakon yadda yake kallon munin matakan Donald Trump, jami'in fafutika Abdu Alhaji Idi ya bukaci shugabanni da magoya bayan jam'iyyar Republican su takawa shugaban na Amurka birki domin kada ya kara yin tunanen bullo da wasu matakan da ka iya gurbata zamantakewar al'ummomin duniya.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG