Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Adamawa Jami'an Tsaro Na Tatsar Direbobi da Masu Ababen Hawa


Sojoji da 'yansanda dake karban na goro hannun direbobi da masu ababen hawa

Masu ababen hawa da direbobin motocin haya na kokawa da irin tatsar da jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yansanda su keyi masu akan hanya, wato dole sai sun karbi kudi masu yawa kafin su bar mutum ya wuce.

Jami'an tsaron su kan kafa shingaye ne na duba ababen hawa to amma kuma sai su juya suna karban kudade daga hannun jama'a alatilas.

Wakilin Muryar Amurka dake jihar Adamawa ganao ne akan wannan irin mummunan halin jami'an tsaron wadanda tamkar suna yiwa jama'a kwace ne a kan hanya. Shi da wasu 'yan jarida sun bi hanya domin su tabbatar da gaskiyan koken jama'a. Shi da abokansa basu tsira ba domin an ci zarafinsu ta wajen tilasta masu su rabu da kudadensu.

Wakilinmu da abokansa sun tarad da jami'an tsaro da wasu matafiya suna cecekuce akan kudin da jami'an tsaron suka nema a hannunsu.

Wani direba yace kowace rana yana kashe kimanin nera dubu ukku wa jami'an tsaro domin ya cigaba da aikinsa na daukan fasinjoji. Yace dole ka bayar ko kuma su wulakantaka. Hatta fasinjoji ma zasu zagi direban idan bai bayar da kudi ba da sauri. Yace abun da su keyi sai su sauka su je su samesu su yi jinga akan abun da zasu bayar. Su kan yi jingar dari ukku ko hudu kafin su wuce. Haka ma idan sun dawo dole sai sun bada wani abu.

Amma sabon kwamishanan 'yansandan jihar Adamawa Musa Kimo da aka tunkareshi da abun da jami'ansa ke yi sai yace suna kokarin sauyawa wadanda suka dade wurin aiki domin samun nasarar yaki da bata gari. Ya kara da cewa shi da jami'ansa zasu yi aiki tsakainisu da Allah

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG