Accessibility links

A Jihar Gombe 'Yan Sanda Biyu Sun Mutu Wani Matashi Daya Kuma ya Halaka a Kauyen Difa

  • Aliyu Imam

Sojojin Najeriya suke sintiri.

Rikici tsakanin 'Yansanda da wasu matsa yayi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro biyu da farin hula daya.

Rundunar 'Yansanda ta jihar Gombe tana gudanar da bincike kan rahotanni da suke nuni d a cewa 'Yansanda biyu sun halaka wani matashi daya kuma ya rasa ransa sakamakon yunkurin da jami'an tsaron suka yi na kama wasu matasa.

Rahotanni da muke samu daga kauyen Difa cikin karamar hukumar Yamaltu Deba, sun ce 'Yansandan sun kama wasu matasa, amma yaran suka ce basu 'yarda ba.

Wani wanda yayi magana da wakilinmu Abdulwahab Mohammed daga Gombe yace 'Yansanda sun yi kokarin gudu, a garin haka ne suka kade matashin ya mutu har lahira. Su kuma 'Yansandan gaba kadan kusa da kasuwar kauyen motarsu ta fada cikin magudanan ruwa.

A wani gefen aka ce motar sai ta kama da wuta ta kona jami'an tsaron, a wasu ruwayar kuma, cewa aka yi matasan da suka bi motar ne suka cunna mata wuta.

kakakin rundunar 'Yansandan jihar DSP Attajiri yace bashi da cikakken bayani amma hukumar tana gudanar da bincike.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG