Accessibility links

Halin da Tsaro Ya Shiga a Arewacin Najeriya Abun Tsoro ne


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Gwamnonin arewacin Najeriya a taron da suka yi a Kaduna sun koka da halin da tsaro ya shiga a yankunansu.

Taron kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da suka yi a Kaduna ya koka da irin halin da harkar tsaro ta shiga a yankin.

Gwamnonin sunn ce halin da tsaro ya shiga a arewacin kasar abun tsoro ne matuka. Sabili da haka gwamnonin sun ce ya kamata gwamnatin tarayya ta kara dagewa domin ta tabbatar da tsaro a arewacin kasar ta Najeriya. Shugaban kungiyar gwamnonin gwamna Muazu Babangida Aliyu na jihar Neja yayi karin bayani game da abun da kungiyarsu ta tattauna. Yace "Abun ya tsoratamu, ya kara tsoratamu domin da muna ganin kaman an kaiga karshe game da maganar Boko Haram sai muka ga kuma kullum yanda abubuwan ke tasowa. Na daya mun dubi cewa yakamata a kara yawan sojoji a kara masu yawan kayan aiki kuma a tabbatar da cewa suna jin dadin aikinsu. Su kuma mutane dake nan kasa sai muka ce to dole a san yadda zamu kamosu a tabbata cewa jama'a na tare da gwamnati ta bada abun da yakamata mu sani. To in Allah Ya yadda a yadda muke tsammani lalle zamu kaiga gafi a wannan al'amari musamman 'yan canje canje da aka yi da kuma cewa ita gwamnatin tarayya zata taimaka kwarai. Kuma mun ce su kansu gwamnatocin jihohin nan guda uku a kara taimaka masu da kudade kar a barsu kawai suna yin anfani da kudadensu."

Gwaman Babangida Aliyu ya cigaba da cewa "Mun yi maganan Fulani na musamman. Abu biyu, daya yakamata kasashenmu yanzu mu tabbatar mun bada abunbuwan da zai sa bafillatani ba dole sai ya kwashi shanunsa yana ta yawo kasa ba. Na biyu yanzu sai gashi da yake an bar satan banki yanzu kuma sai gonakin shanu ake bi ana sacewa. Mun lura kamar akwai hadi tsakanin abun dake faruwa na rashin zaman lafiya da kuma sace-sacen nan. Muka ce to dole ne a yi wani abu don mu tabbata a san me ake ciki."

Gwamnan Kano Dr Rabiu Kwankwaso na cikin gwamnonin da suka halarci taron shi ma ya yi karin haske dangane da taron nasu, inda yace "Mun gane yanzu ana kashe kudade da yawa kuma ana batawa mutanenmu lokaci da yawa a kan hanya zuwa kai abinci kasashen kudu wannan shi ya sa muka dauki mataki muka tarda cewa kowa ya tafi ba tare da bata lokaci ba a tsayar da wannan. Mu dama a Kano mun samu labari mun tsayar kuma dukanin gwamnonin nan kowa ya yadda mutanenmu ne suke sayo kayayyakin nan. Mutanenmu ne suke sayarwa kuma mutanenmu ne suke saya a kudu. Babu dalilin da za'a sa haraji wannan ya biya a nan wannan a biya anan. Mutanenmu a kan hanya ana ci masu mutunci ana bata masu lokaci, tattasai na lalacewa tumatiri na lalacewa wannan gwamnoni sun yadda ba zamu yadda da shi ba a koina"

Masu safarar kayan abinci da dabbobi sun furta jin dadinsu da matakan da gwamnonin suka dauka. Alhaji Muhammed Tahir Ibrahim shugaban hadaddiyar kungiyar masu safarar abinci da dabbobi yace "Dama abun da muke jira ke nan yau shekara shida. Allah Subuhana Wata'ala yau Ya Kawo mana. Yanzu ka duba daga Maiduguri zuwa Legas zaka kashe nera dubu dari biyu da tamanin. Daga Sokoto zaka je Benin zaka kashe nera dubu dari biyu da talatin...To jarin mutanenmu ya riga ya kare domin mai sayen mota biyu da yau baya sayen mota daya....Ana neman a karya mana arzikinmu a arewa gaba daya sabo dashi ne muka kawo kuka a gaban gwamnonin arewa"

To sai dai taron gwamnonin ya samu rauni domin a cikin gwamnoni goma sha tara shida kawai suka samu halarta. Wasu ma ko wakili basu aiko ba.

XS
SM
MD
LG