Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kalla Masu Zanga Zanga 17 Ne Suka Rasa Rayukansu A Congo


Masu Zanga Zanga a Birnin Kinshasha

Rundunar ‘yan sanda a Jamhuriyar Demokaradiyar Congo tace a kalla mutane 17 ne suka mutu a lokacin zanga-zanga na kiran shugaba Kabila ya yi murabus.

Rundunar ‘yan sanda a Jamhuriyar Demokaradiyar Congo tace a kalla mutane 17 ne suka mutu a lokacin zanga-zanga na kiran shugaba Kabila ya yi murabus.

Jami’ai sun ce wadanda suka mutu sun hada da yan sanda uku da fararen hula 14. An fara rikicin ne da safiyar jiya Litinin yayinda ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar taruwa a birnin Kinshasa.

Wadansu shaidu sun ce masu zanga-zangar sun jefi yan sandan da duwatsu kuma sun kona tayoyi da motoci, a yayinda ‘yan sandan suka yi amfani da barkono tsohuwa a kan masu zanga-zangar.

Da rana sai aka tura yan sanda da sojoji suka tare hanyar da zata kai masu zanga-zangar ga inda zasu taru dake kusa da ginin majalisar dokin kasar.

Wakilin Muryar Amurka ya ga jami’an tsaro sun dakatar da wasu mutane shida da yake zato masu sa ido ne daga kasar waje kuma aka daukesu da mota.

Yan adawa suna zargin Shugaba Kabila da yunkurin karawa kansa wa’adin shugabancin kasar inda yake jan kafa wurin shirya zabe, wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Magoya bayan shugaban kasar sun musunta zargin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG