Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kamaru Ana Ba Matasa Jari Domin Kada Su Shiga Kungiyar Boko Haram


Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya

Boko Haram daga Najeriya tana ci gaba da neman magoya baya daga kamaru. Gwamnatin kamaru da wata kungiyar agaji mai zaman kanta ta kasa-kasa, sun fara baiwa matasa a yankin tallafin dabbobi domin su taimaka musu su sami abun dogaro, kuma hakan ya hana su shiga kungiyar ‘yan ta’addan.

Issa Yeguie, dan shekaru 29 da haifuwa, yace yanzu shekara daya kenan bai ga danuwansa kadai da yake da shi ba, tun bayan da wasu baki suka ziyarce su a kauyensu, suka yi musu tayin zasu basu albashi mai tsoka ko wani wata, idan suka shiga kungiyar Boko Haram.

Issa bai karbi tayin ba, yanzu yana lura da gonan kajinsa a kauyen Zamai, kusa da garin Mokollo dake arewacin kasar. Ya fara kiwon kajin ne daga tallafin kaji da gwamnati ta bashi da kuma shawarwari kan kiwon da noma daga wani ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD. Saboda haka yanzu, Issa yace yana iya daukar nauyin matarsa da ‘yayansa uku da kuma mahaifiyarsa ‘yar shekaru 72 da haifuwa.

Yace yanzu yana da kawarin guiwa, kuma ba tareda wata kumbiya-kumbiya ba, da kwai haske a gaba. Yanzu yana da ‘yan tsaki 60 daga kaji tara da aka bashi,kuma abokansa sun daina zaginsa cewa ya kasa ciyarda iyalinsa.

Issa yana daga cikin daruruwan mutane da suke amfana karkashin wani shirin MDD na horasda matasa su kaucewa shiga Boko Haram, kungiyar da take kai hare hare cikin shekaru da suka wuce a arewacin kamaru.

Mai kula da shirin na MDD Najad Rochdi, tace burin shine tallafawa tattalin arzikin yankin duk da tarzoma da ake ci gaba da fuskanta.

Ganin yadda rashin tsaro ya addabi yankin a gefe daya, a daya bangaren kuma ga mummunar tarzoma, tilas ne a samar da yanayi na farfado da tattalin arzikin ta wajen dogaro da kwarewar mutanen da suke zama can, kuma babban abunda aka kware akai shine noma, saka, da kiwo, da kuma bude cibiyoyin cinikayya ko kasuwanni da zai kasance dandalin haduwa ga dukkan mazauna yankin.

Kamaru ta samar da dala milyan hudu a zaman tallafi na gaggawa domin a samar da ayyukan yi ga matasa a arewacin kasar dake kan iyaka da Najeriya, inda rashin ayyukan yi ya kai kashi 90 cikin dari na mazauna wurin. Japan ta bada gudumawar dala milyan biyu ga MDD domin kashi na biyu na wannan shiri, wanda zai maida hankali ga illahirin yankin kasar da rikicin ya shafa a kamaru.

Mal Ibrahim Hamawa, shine hakimin Zamai, yace shirin tallafin ya rage zaman kashe wando tsakanin jama’arsa su dubu 30.

Yace ya godewa shirin na MDD da gwamnatin kamaru na bullo da shirin dogaro da kai, ta wajen gina kasuwar dabbobi domin samar da kayayyakin abinci masu gina jiki domin ‘yan kasar da aka tilastawa barin muhallansu, da kuma ‘yan gudun hijira daga wasu wurare, kuma ta haka-suka bunkasa tattalin arzikin yankin, da inganata rayuwar manoman da masu kiwo a yankin.

Kamar mita dari daga gonar kajin Issa Yeguie, sai lambun Hamza Falama, inda yake ban ruwa.

Yace lokacin damina suna noma masara da dangin hatsi, lokacin rani kuma su shuka karas, da ganyen lettuce, wanda ta hake suke samun kudin tura yara makaranta, su kula da lafiyar iyali, da cimaka da kuma a adana wani abu domin bacin rana.

Kamaru tana fatan ganin Karin lambuna a arewacin kasar, domin karya gadon bayan Boko Haram a yankin.

Ga karnin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:26 0:00

XS
SM
MD
LG