Majalisar Dattawan Amurka, jiya Alhamis, ta tabbatar da Gina Haspel a matsayin mace ta farko da za ta Shugabancin Hukumar Leken Asirin Tsaron Kasar Amurka ta CIA da kuri’u 54 akasin 45, wanda ya kawo karshen tantancewa mai cike da takaddama, inda ‘yan Majalisar Dattawan su ka yi ta nuni da amfani da hanyoyi masu tsanani da hukumar ta CIA ta yi wajen zakula bayanai a baya.
‘Yan jam’iyyar Dimokarat 6 sun kada kuri’ar zaben Haspel, a yayin da wasu ‘yan Republican biyu kuma su ka ki zabenta a matsayin maim aye gurbin Mike Pompeo, wanda a watan jiya aka tabbatar da shi a matsayin Sakataren Harkokin Waje.
Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dattawa Mitch McConnell, dan Republican mai wakiltar Kentucky, ya jinjina ma Haspel, wadda dadaddiyar ma’aikaciyar CIA ce, da cewa ta yi, “matukar cancanta ta fuskanci kalubale mafi tsanani da Amurka ke fuskanta,” ya kara da cewa ta,”na da mutunci da kuma daraja a idon ma’aikatan hukumar ta CIA.
Takaddama ta barke bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da sunan Haspel a matsayin wadda ya ke so ta shugabanci hukumar ta CIA, saboda yadda ta jagoranci tsarin gwale-gwalen da hukumar ta yi amfani da shi wajen tatsar bayanai bayan harin ta’adancin da aka kai ma Amurka a ranar 9 ga watan Satumba na 2001, wanda aka fi sani da 9/11.
Facebook Forum