Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Mahaifiyar Shekau Ta Yi Magana - Chika Oduah


Mahaifiyar Abubakar Shekau, Falmata Abubakar
Mahaifiyar Abubakar Shekau, Falmata Abubakar

Mahaifiyar Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ta tattauna da Muryar Amurka inda ta bayyana cewa ta yi shekaru 15 ba ta ganshi ba.

A kauyen Shekau da ke Jihar Yobe, dattawa da shugabannin al’umma sun kai Muryar Amurka wajen Falmata Abubakar wadda suka ce ita ce mahaifiyar Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. Mahaifinsa limamin kauye ne gabanin rasuwarsa a wasu ‘yan shekaru da suka gabata.

Falmata ta ce ba ta taba magana da ‘yan jarida ba kafin Muryar Amurka kuma ba ta da masaniyar inda ya ke ko halin da ya ke ciki.

“Ko ya mutu, ko yana nan da ransa ne, ba ni da masaniya. Allah kadai ya sani. Shekaru na goma sha biyar kenan tun da ganinsa,” inji ta.

Suna Boye Kauyensu

Mutanen garin sun bayyana cewa sau da yawa su kan boye cewa sun fito daga gari daya da Abubakar Shekau domin gudun a ce suna da alaka da kungiyar Boko Haram.

Falmata ta ce a lokacin da ya ke yaro karami, Abubakar ya tafi Maiduguri domin karatun addinin Islama. Inda ya kasance almajiri kuma ba mamaki ya yi yawon bara akan titunan Maiduguri.

A cewarta, a yayin karatunsa ne har ya hadu da Mohammed Yusuf, wanda ya kirkiri Boko Haram bayan yin watsi da ilimin boko da kuma ayyanashi a matsayin haramun. Falmata ta ce a nan ne aka sauyawa danta tunani.

Ya Sauya

“Tun da Shekau ya hadu da Mohammed Yusuf, ban sake ganinshi ba,” inji Falmata

“Na san dana ne, kuma kowa ya san son da uwa ke wa danta, amma halayenmu sun sha banban,” inji ta. “Ya jefa mutane da dama cikin bala’i. Ina ma zan ganshi domin in ja hankalinsa? Ya jefa jama’a da dama cikin tashin hankali, amma ina rokon Allah ya shiryeshi.”

Shekau ya jagoranci kungiyar da ta kashe mutane sama da dubu 30 tare da sace mutane a yankunan Arewa maso gabas da tafkin Chadi.

Haka kuma kungiyar ta lalata makarantu sama da 1400 a cewar Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Falmata ta ce ba za ta tsine masa ba, amma ya rikida ya zama wani can ta ba ta sani ba.

Ta kara da cewa, “Ya dauki wata tarbiyya can ba wadda na koya masa ba. Allah ne kadai ya san dabi’ar da ya dauka.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG