Accessibility links

A Karon Farko Majalisar Dokokin Jihar Kano ta Nemi Ra'ayin Jama'a Kan Kasafin Kudi


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Jihar Kano ta yi abun da ba'a taba yi ba aduk fadin Najeriya yayin da najalisar dokokin jihar ta nemi ra'ayin jama'a kan kasafin kudin jihar

Karon farko ke nan da majalisar dokokin jihar Kano ta shirya taron masu ruwa da tsaki a jihar domin samun ra'ayinsu kan kasafin kudin jihar na wannan shekarar. Ba'a taba yin irin wannan taron ba na neman ra'ayin jama'a kan dokar kasafin kudi.

Tun watan Disambar bara gwamnan jihar Dr Rabiu Kwankwaso ya mikawa majalisar kasafin kudi na nera biliyan 219 domin ta duba ta mayar dashi doka kamar yadda aka saba yi.

Hamza Sule Bichi shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar ya ce babbar manufarsu ita ce su samu su ji ra'ayin mutane kafin su mayar da ita doka. Ya ce sau da dama mutane sukan ce suna son su bayyana nasu ra'ayin kan kasafin kudin jihar. Akwai wadanda suke son su bayyana bukatunsu domin su suka san abun da suke so. Ya ce zasu tattara ra'ayoyin su ga wadanda suka fi alfanu ga jama'a

Malama Rabiu ita ce ta gabatar da mukala a madadin hadaddiyar kungiyar nakasassu inda ta ce suna bukatan a kara masu taimakon da ake basu domin su kula da lafiyarsu. Suna kuma son ilimi mai inganci da kayan aiki. Ban da haka sun bukaci a mayarda kudurin da suka rubuta doka.

Hajiya Kolo mai rajin bunkasa lafiyar mata da yara kanana ta bayyana abubuwan da yakamata gwamnati ta mayarda hankali a kansu domin inganta kiwon lafiyar yara da mata. Ta fi son a zare masu kadadensu domin su kula da kansu.

Farfasa Garba Sheka masani kan tattalin arziki daga Jami'ar Bayero ya ce kodayake gwamnati na kokarin taimakawa jama'a ita majalisar dokoki ya kamata ta yi gyara ga kasafin kudin.

XS
SM
MD
LG