Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Tun Hawa Mulki Mataimakin Trump Yana Ziyara a Turai


Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, a karon farko tun bayan da ya kama aiki, yana ziyara a Turai.

Mike Pence dai ya kai ziyarar ne domin tabbatarwa kawayen Amurka cewa, har gobe Washington zata ci da zama babbar kawa, a dai dai lokacin da kasashen suke nuna damuwa kan kudurin gwamnatin Trump na "saka Amurka akan gaba da komi" a zaman yadda zata tunkari harkokin duniya.

Tuni dai ake jin cewa Pence, yayi zaman cin abincin dare da Fara Ministan Belgium Charles Michel, a jiya Lahadi.

Yau Litinin, ake sa ran mataimakin shugaban na Amurka zai gana ministar harkokin waje da tsaro na kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini, da shugaban kungiyar Donald Tusk, da wasu jami'an kungiyar.

Babu mamaki idan kungiyar ta nemi karin bayani kan hasashen da Donald Trump yayi cikin watan jiya da wasu jaridun Turai biyu suka wallafa kan cewa wasu kasashen turai zasu bi sawun Birtaniya wajen ficewa daga kungiyar ta tarayyar Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG