Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kasar Kwango Kinshasha An Kone Hedkwatocin Jam'iyyun Hamayya


Gawarwakin wadanda aka kashe

Rahotanni daga Kinshasa, sun ce cikin dare an kona helkwotocin jam'iyun hamayya uku,kwana daya bayan zanga zangar nuna kyama ga shugaban kasarJoseph Kabila, ta rikida ta zama tarzoma har mutane 12 suka halaka.

Mutum daya ne ya jikkata sakamakon wutar da ta tashi a babbar helkwatar jam'iyar siyasar kasar kamar yadda jam'iyyar AFP tayi bayani,sai dai babu wanda ya jikkata a helkwatocin jam'iyun FONUS, ko MLP dukkansu a babban birnin kasar Kinshasa.

Wuta ta tashi ne bayan wata mummunar zanga zanagr da 'yansanda suka ce ta halaka mutane 17.

Jami'an kasar suka ce cikin wadanda suka halakan har da 'yan sanda uku da farar hula 14.Tarzomar ta barke ne jiya Litinin, bayan da 'Yansanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar haduwa a birnin na Kinshasa.

Wasu shadun gani da ido suka ce wasu masu zanga zanga sun cunnawa tayoyi da motoci wuta, su kuma 'Yansanda suka harba borkonon tsohuwa da kuma albarusai kan masu zanga zangan.

XS
SM
MD
LG