Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kwai Bukatar Kai Daukin Gaggawa Inji Kungiyar Likitoci


Kungiyar likitocin masu bada agaji kyauta da ake kira da turanci Doctor Without Borders, sun bukaci akai ‘daukin gaggawa ga wasu bayin ALLAH a jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Najeriya wadda tayi fama da ‘yan boko haram.

Kungiyar tace yanzu haka akwai a kalla mutane da yawan su ya kai dubu dari biyar da suke cikin matsananciyar bukatar abinci, da kiwon lafiya, da ruwan sha da kuma wurin kwana nagari.

Kungiyar tace wajibi kungiyoyi masu zaman kansu su mike tsaye domin bada agajin gaggawa a wannan sansani.

Babban darekta mai kula da harkokin yau da kullun na kungiyar ce Dr Isabelle Defouny ta fadi haka a jiya laraba.

Kungiyar tace yayin da sojojin Najeriya tayi nasar fatattakar ‘yan kungiyar boko haram yanzu abinda ya fito fili shine tsananin rayuwar kunci da wadannan bayin ALKLAH da suka samu kansu a wannan yanki ke fama dashi.

Kungiyar tace da yawan su sun kasance a kebe da sauran sassan duniya na kusan tsawon shekaru biyu basu san meke faruwa a wasu sassan duniya ba.

Sai dai wadannan bayin ALLAH da yanzu haka suke karkashin kulawar sojoji a sansanoni daban-daban suna matukar famma da rashin cimaka.

Kungiyar tace ko a cikin watan jiya sai da ta samu yara har su 16 da suke daf da mutuwa sakamakon rashin abinci a sansanin yan gudun hijirar dake Bama inda suka umurci akai su wurin ciyar da mutane domin a ceto ran su.

XS
SM
MD
LG