Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kwai Yiwuwar Bullar Wata Babbar Jam’iyya Idan Ba a Samu Hadin Kai A PDP Ba


PDP

Bangarorin PDP biyu na zargin juna da kafa wata sabuwar jam’iyya mai taken MEGA Party da zata fafata da APC a babban zaben Najeriya na shekara ta 2019.

Shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar PDP Sanata Walid Jibrin, yace baya tare da duk wani mai tunanin koda canza sunan PDP ne balle ma aje ga batun kafa wata sabuwar jam’iyya.

Sai dai kuma kakakin bangaren Sanata Modu Sheriff, Inuwa Bala, yace bangaren Makarfi ne ka kawo wannan batun don neman sake kawo rudani a cikin jam’iyyar, kuma wannan wani take-take ne na yunkurin komawa wata jam’iyya.

Sakataren shirye shirye na kwamitin rikon PDP, Abdul Ningi, na ganin har yanzu akwai ‘rina a kaba’ domin wannan fadan shine babban abin da yake kawo koma baya ga jam’iyya. Ya kuma ce sun tabbatar cewa akwai hannun baki a ciki.

Masana siyasa na ganin ko dai PDP bata hade ba akwai yiwuwar bullar wata gagarumar jam’iyyar adawa da manyan ‘yan siyasar da na ciki na ciki tsakaninsu da gwamnatin APC zasu kafa. Tun rikicin bangarewar PDP har yanzu hedikwatar jam’iyyar Wadata Plaza na rufe da ‘yan sanda na gadi.

Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG