Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar, Nakasassu na Yunkurin Aika Wakilansu Majalisun Kasar


Wasu alkaluman da ba na hukuma ba sun kiyasta cewa daga cikin mutane miliyan 17 na yawan al’ummar Nijar, adadin masu fama da nakassa ya haura miliyan daya. Abin da ya sa kungiyoyinsu ke ganin akwai bukatar dagewa domin aika wakilansu a majalisun Kasar.

Shugabannin kungiyoyin nakasassu na ganin zabukan shekarar 2016 da za a yi a matsayin wata dama ta gyaran kurakuran da aka yi a zabukan da suka gabata, inji Malam Ila Iro, wani kusa a kungiyar nakasassu ta kasa. Ya ka ra da cewa suma ‘yan kasa ne kuma suna kokarin ganin nakasassu a fannonin al’umma daban daban.

Samun ilimi wani ‘yanci ne da doka ta ce waijbi ne kowanne dan kasar Nijar ya mora, to sai dai matsalar karatu na daya daga cikin kalubalen da masu fama da nakasa ke fuskanta.

Madam Ibrahim Fati Bubakar, shugabar Mata guragun Nijar, ta fadawa wakilin sashen hausa Sule Mummuni Burma cewa ‘yayan nakasassu ma ba a bar su a baya, ko a makarantu ana tsangwamarsu, ana kyamarsu. Ta kuma ce wani lokaci kuma ana tauye wa ‘yayansu hakkokinsu, ko da su na da hazaka sai ka ga ‘yayan masu hannu da shuni da ba su kai su kokari ba sun mamaye ko’ina.

Madam Fati Bubakar ta kara da cewa yanzu kam kansu ya waye don sai inda karfinsu ya kare wajen kare hakkokin ‘yayansu.

Yau sama da ‘yan shekaru ke nan da nakasassu suka yi watsi da sana’ar bara domin rungumar sana’o’in hannu a Nijar, sai dai nakassasun sun koka akan cewa hukumomin kasar ba sa sayen abubuwan da suke sarrafawa.

Ga cikakken rahoton daga Sule Mummuni Burma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG