Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kaiwa Tawagar Gwamnan Borno Hari


Gwamnan Borno Babagana Zulum
Gwamnan Borno Babagana Zulum

Wasu mahara da ba a tantance ba, sun yi wa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Zulum kwantan bauna tsakanin garin Monguno da Baga, suka kashe jami’an tsaro goma sha daya da suka hada da sojoji da ‘yan sanda, da kuma a kalla membobin kungiyar sintiri da ake kira Civilian JTF 2.

Majiyun Muryar Amurka sun bayyana cewa, gwamnan ya je Baga ne domin ci gaba da shirye shiryen maida ‘yan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali, wadanda kungiyar Boko Haram ta raba da muhallansu tun 2014, bayan kafa kwamitin makonni biyu da suka gabata, karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar shari’a na jihar Barrister Kaka Shehu Lawan.

Bisa ga majiyun harin bai hana gwamnan da tawagarsa isa Baga ba, inda suka kwana domin ci gaba da wannan shiri.

gwamnatin-barno-za-ta-maida-yan-gudun-hijran-baga-mazauninsu

gwamnatin-borno-ta-fara-maida-yan-gudun-hijira-gida

zulum-ya-ce-harin-da-aka-kai-kan-tawagarsa-zagon-kasa-ne

Shi dai gwamnan ya tafi Baga ne ta jirgi mai saukar angulu yayinda tawagar tasa suka tafi ta hanyar mota.

Maharan da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai wa tawagar harin ne a kauyen Cross Kawa da ke kusa da barikin sojan hadin guiwa da ya kunshi sojojin kasashen Chadi, Kamaru, da Nijar.

Idan ba a manta ba, kwanaki hudu da suka gabata, aka kaiwa jami’an sojoji hari a Damboa aka kashe babban kwamandan soja na garin Kanar Dahiru Bako.

Wannan ne karo na biyu da ake kaiwa tawagar gwamna Babagana Zulum hari cikin shekara guda.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG