Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Barno Za Ta Maida Yan Gudun Hijran Baga Mazauninsu


Dr. Babagana Umar Zulum
Dr. Babagana Umar Zulum

Gwamnatin jihar Barno da ke Arewa Maso Gabashin Najeria ta kafa kwamiti mai wakilai 23 da zai yi aikin tantance ‘yan gudun hijiran Baga da yanzu haka ke karamar hukumar Kukawa sanadiyar tarwatsa garin da mayakan Boko Haran suka yi a ‘yan shekarun baya.

Da yawansu da yanzu haka suna samun mafaka ne a sansanonin ‘yan gudun hijira dake garin Maiduguri, za’a maida su garinsu na Baga bisa tabbacin da jami’an tsaro suka ba gwamnati na samun zaman lafiya.

Baga dai gari ne da ke da harkokin kasuwancin kasa-da-kasa kuma ya ke gabar tafkin Tchadi. Wannan yasa masunta da manoma da dama suke gudanar da harkokinsu da makwabtansu cikin lumana kafin ‘yan shekarun baya da wasu da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka tarwatsa garin, sannan daga bisani Jami’an tsaro suka kwato garin daga hannu mayakan.

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, yace, “Bayan da na kai ziyarar gani da ido ran 5 ga watan domin gane wa kai na halin da garin ke ciki, na rubuta wa babban hafsan sojin Najeria, na bayyana masa niyarmu ta maida ‘yan gudun hijiran garinsu, ya kuma yi na'am da haka.”

Gwamnan ya kara da cewa kwamitin zai kula da abubuwan da suka dace harma da lamurran da suka shafi lafiyar jama'ar da dukiyoyinsu, kuma zai maido da harkokin fararen hula da tantance yan gudun hijiran da za’ayi musu tanadin komawa.

Kaka Shehu Lawan, Kwamishinan Sharia na Jihar shine shugaban Kwamitin. Yace, “ da farko dai za’a je Baga a duba abinda ya kamata ayi wa mutanen. Magudanan ruwa za’a gyara, tunda yanzu damina ne kuma za’a gyara musu gidajensu, da asibitoci duka za’a gyara. Bayan nan kuma me ya kamata ayi musu, abinci ya kamata a ba su, kayan sawa ya kamata aba su ko sana’a?’

Ya kara da cewa, “dukkan wadannan za mu duba kafin mu baiwa gwamnati shawara kafin gwanati ta yi abin da ya kamata. Kuma za mu hada kai da jami’an tsaro tunda su ma suna cikin kwamitin, domin mu tabbatar da ba’a sake shiga Baga an gudanar da ta’addanci ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG