Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Saliyo Zaizayar Kasa Ta Yi Sanadiyar Rayuka Sama Da 400


Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin zaizayar kasa a Saliyo na ci gaba da karuwa, yayin da yawan ruwan sama ke kawo cikas ga aikin ceton wadanda suka bata.

A yau Juma’a Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan mutanen da suka mutu dalilin zaizayar ‘kasa a Saliyo ya karu inda ya kai sama da 400.

Aikin neman wasu mutane 600 yayi wahala a dalilin ruwan sama, wanda hasashe ke nuna cewa za a ci gaba da yi har na tsawon wasu kwanaki masu zuwa.

Shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koromo, ya mika ta’aziyyarsa da kuma goyon bayan taimakawa a wajen jana’iza da akayi jiya Alhamis.

Yace “Muna bukatar mu hada kai domin jimamin wannan masifa da ta samemu a kasarmu, ta ambaliyar ruwa da kuma zaizayar ‘kasa, wannan wani lamari ne mai zafin gaske ya samemu a tarihin kasarmu. Ruwa ya share daruruwan mutane lokacin da suke barci zuwa mutuwa.”

Gwamnati ta sha wahala wajen ceton mutanen da suka ‘ki bin umarnin gargadin da aka yi musu da cewa su bar gidajensu, bayan wani gargadin da ya biyo baya na cewa an sami wata katuwar gocewar ‘kasa da zata harfar da zaizaya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG