Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Za a Buga Muhawarar Farko Tsakanin Trump Da Biden


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.
Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Amurkawa sama da miliyan 100 ake kyautata zaton za su kalli muhawarar farko tsakanin Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden na Jam'iyyar Demokarat.

Shugaban Amurka, dan jam’iyyar Republican, Donald Trump da mai kalubalantarsa a jam’iyyar Demokarat, tsohon Mataimakin Shugaban kasa Joe Biden, na shirin buga muhawara da daren yau dinnan Talata, makwanni hudu gabanin zaben da za a gudanar ranar 3 ga watan Nuwamba, wanda shi ne na farko a jerin muhawarori uku da za su yi gaba da gaba, cikin watan gobe.

Wannan al’amari mai matukar muhimmanci, wanda za a yi a birnin Cleveland na jahar Ohio, na zuwa ne a daidai lokacin da Biden ke gaba da Trump da maki 7 a kuri’ar jin ra’ayin jama’a a fadin kasar, wanda ke barazanar mai da Trump shugaba na uku cikin shekaru 40 da ya kasa samun wa’adi na biyu na shekaru hudu.

To saidai su na kurkusa ne a da dama daga cikin jahohin da su ka fi muhimmanci wurin cin zabe, wanda hakan na iya sawa ko da Trump ya kasa cin jimlar kuri’u mafiya yawa – kamar yadda ya faru a karawarsa da Hillary Clinton ta Demokarat a 2016 – ya ci kuri’un jahohin da su ka fi muhimmcin wurin cin zabe din, ya kuma yi nasara.

An kiyasta cewa Amurkawa miliyan 100 ne za su kalli wannan bugawar da ‘yan takarar Shugaban kasa za su yi ta tsawon minti 90.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG