Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Nemi Biden Ya Yi Gwajin Kwayoyi


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.
Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa zai bukaci abokin takararsa na jam’iyar Demokrat a babban zaben uku ga watan Nuwamba, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da yayi gwajin kwayoyi kafin ko bayan muhawararsu ta ranar Talata.

Shugaba Trump ya ce ya fadi hakan ne saboda Biden ya kasa tabuka wani abu a muhawarorin siyasa da suka gabata saboda an ba shi wani abu mai bugarwa.

Zargin na Trump da ba saban ba, da yayi a ‘yan makwannin nan na zuwane yayin da ya ke ci gaba da bin bayan Biden a zaben jin ra’ayoyin jama’a wanda ya kasance a haka na tsawon watanni.

Trump na fuskantar yiwuwar zama shugaban Amurka na uku a cikin shekaru 40 da zai gaza sake cin zaben wadi na biyu na tsawon shekara hudu.

Trump mai shekaru 74, na yawan bayyana tababa akan lafiyar kwakwalwar Biden mai shekaru 77.

To amma a lokuta da dama Biden ya kan yi dariya idan yaji zargin na Trump, yana jaddada cewar zai fafata sosai da Trump har ma ya dara shi a muhawarar.

A wata hira da matar Biden Jill a gidan talabijin na CNN a jiya Lahadi, ta ce, “a shiye yake. Abin da yake faranta mini rai shine sanda Amurkawa zasu ga Joe Biden akan mumbari”

Trump da Biden zasu fafata muhawara har sau uku a wata mai kamawa, farawa da ta ranar Talata na tsawon mintuna 90, da dan jarida Chris Wallace na Talabijin din Fox News zai jagoranta daga tsakiyar birnin Cleveland na Jihar Ohio.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG