Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abdullahi Adamu Da Akasarin ‘Yan Takarar Shugabancin APC Sun Yi Nasara Ba Tare Da Kada Kuri’a Ba


Sabon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu

Karshe dai tsohon gwamnan jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu da akasarin ‘yan takara a babban taron jam’iyyar APC, sun samu nasara ta hanyar daidaitawa, ba tare da kada kuri’a ko daya ba.

An samu wasu ‘yan takara ‘yan kalilan na shiyya da su ka ce su na bukatar a gudanar da zaben, amma su din ma yawanci gwamnoni sun rarrashe su su ka janye.

Daya bayan daya masu takara su ka rika janyewa don mara baya ga jerin sunayen da gwamnoni su ka amince da su da a ciki akwai wanda a ka yi amanna dan takarar shugaba Buhari ne, wato sabon shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Gabanin tabbatar ma sa nasarar, Sanata Adamu ya ce ai ba ya shakkar a shata dagar zabe.

Na ji a na ta sharhi a taron cewa in ka debe Abdullahi Adamu sauran shugabannin gwamnoni su ka ba da sunayensu da kauce wa jerin sunayen da shugaba Buhari ya amince da su.

Hakan bijire wa shugaba Buhari ne ko kuwa a’a, shugaban ya fice daga dandalin taron ba tare da shaida yanda a ka yi ta janyewa ba da nuna don mutunta shugaban ne.

Gwamnoni ne su ka dora jama’arsu a karagar jam’iyya da ke nuna alamar haka za su sake yi a tsaida dan takarar shugaba da ba lallai sai wanda shugaba Buhari ke kauna ba.

Shin APC ta bar baya da kura ko an yayyafa wa kurar ruwa?

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG