Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abdulrasheed Bawa Ya Samu Sauki - EFCC


Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Facebook/EFCC)
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Facebook/EFCC)

Rahotanni sun ce shugaban na EFCC ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro.

Hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce shugabanta Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya.

EFCC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook mai taken “Bawa na cikin koshin lafiya.”

A ranar Alhamis rahotanni daga Najeriya sun ruwaito cewa shugaban na EFCC ya yanke jiki ya fadi a fadar ta shugaban kasa, lamarin da ya sa ya dakatar da jawabin da yake yi a lokacin.

“Ya zama dole mu fito mu yi karin haske, bayan wani lamari da ya faru a ranar 16 ga watan Satumba, 2021 a fadar shugaban kasa a Abuja a lokacin yana gabatar da jawabi a bikin ranar shaidar dan kasa, inda ya ji ba ya jin dadi, hakan ya sa sai da ya koma kujerarsa ya zauna.” Sanarwar ta ce.

Sai dai jim kadan bayan aukuwar hakan, hukumar ta EFCC wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce Bawa yana cikin koshin lafiya.

“Tuni aka kula da lafiyarsa, kuma yana shirin komawa bakin aiki.” Sanarwar ta ce.

XS
SM
MD
LG