Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hushpuppi: EFCC Ta Karyata Mompha


EFCC
EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya – EFCC ta musanta ikirarin ma’aboci shafin yanar gizo na Instagram, Ismaila Mustapha, cewa hukumar ta shawarce shi da ya rage kwaramniya.

A wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar, ta bayyana cewa Ismaila Mustapha ya yi karya a ikirarin da yayi na ce hukumar ta ba shi shawarar ya daina yawan bayyana kansa a cikin al’umma.

Mustapha wanda aka fi sani da Mompha, ya yi da’awar cewa hukumar ta ba shi shawarar ya dan lafe, biyo bayan kama abokinsa Ramon Abbas wanda aka fi sani da Ray Hushpuppi, da jami’an tsaron kasar Amurka suka yi.

To sai dai hukumar ta EFCC ta ce sam ba ta ba da shawara ga wadanda ake tuhuma da aikata manyan laifuka.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Facebook/EFCC)
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa (Facebook/EFCC)

A cikin sanarwar, mai Magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren, ya ce babu wata alaka ta sadarwa ko tattaunawa da ta wakana tsakanin jami’an hukumar da Mompha, wanda yanzu haka ake masa shari’a kan tuhumar almundahanar kudade a jihar Legas.

Sanarwar ta kara da cewa “kasancewar a cikin ikirarin na Mompha, ya kasa bayyana ko a wane ofishin hukumar ne aka ba shi shawarar, da kuma wanene ma ya ba shi shawarar, ya isa shaida cewa kalaman na sa kirkirarren labari ne da ya kamata a yi watsi da shi.”

Mompha da kamfaninsa Ismalob Global Investment Limited, suna fuskantar shari’a a wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birini Legas.

Mustapha Mompha
Mustapha Mompha

Hukumar ta EFCC ce ta gurfanar da su bisa caje-caje 22, da suka hada da tuhumar zamba da mallakar kudade ta haramtacciyar hanya.

EFCC ta gabatar da shaidu 10 a yayin da ta kammala bayan ta na shigar da kara, to amma kuma a maimakon shiga kariya, sai Monpha ya gabatar da bukatar kotu ta soke karar don bai aikata laifi ba.

To sai dai kotun ta yi watsi da karar ta shi, inda kuma ta bukaci ya kare kan sa akan tuhumar da ake yi masa.

XS
SM
MD
LG