Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Atiku Ya Fada a Wajen Kaddamar Da Yakin Neman Zabensa


Dan takarar shugaban aksa Atiku Abubakar a wajen gangamin yakin neman zabensa a Sokoto

“An ce mana mu jam’iyar PDP ba mu da magoya baya a arewa maso yamma, wadannan ba jama’a ba ne.? In ji Atiku.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce daruruwan magoya bayan jam’iyyar ta PDP ne suka hallara a filin taron da aka kaddamar da yakin neman zaben na PDP.

“An ce mana mu jam’iyyar PDP ba mu da magoya baya a arewa maso yamma, wadannan ba jama’a ba ne.? In ji Atilku

Ya kara da cewa, “abin da ke gabanmu shi ne, zabe tsakanin kawar da talauci da rashin zaman lafiya da rashin aikin yi.”

Daga cikin gaggan jam’iyyar ta PDP da suka halarci taro, akwai tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa.

Atiku zai yi tarkara ne da shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabrairun badi, duk da cewa akwai wasu 'yan takara a sauran jam'iyyun kasar.

Tun kusan makwanni biyu Buhari ya kaddamar da na sa yakin neman zaben.

Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna domin jin jawabin Atiku:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG